Aminu Ado Bayero Ne Sabon Sarkin Kano Bayan Tunbuke Sarkin Sanusi Lamido

0
1055

 

Zubair Sada Da Mustapha Imrana Abdullahi

AN sami sabon Sarkin Kano, wanda zai ci gaba da sarautar masarautar mai dimbin tarihi. An nada Alhaji Aminu Ado Bayero sabon San Kano ne bayan da Majalisar Zartaswar Jihar Kano ta amince da sauke Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi daga sarautar, a wani zama na musamman da majalisar ta yi a yau Litinin 9 ga watan Maris, 2020.

Sabon sarkin dai ya zama na daya a wajen zaben ne wadanda majalisar zartaswar da nada sabon sarki ta yi ga magadan kujerar ta sarkin Kano, inda sauran ‘yan uwa suka yi masa mubaya’a ba tare da bata lokaci ba.

Kafin dai cire shi tsohon sarki Sanusi Lamido, akwai lamarin tayar da cibiyoyin wuta a majalisar dokokin Jihar game da lamarin a ranar Litinin. Lokacin rubuta wannan labarin tuni aka girke jami’an tsaro a majalisar da sauran wuraren da ake tanmahan za a iya samun barkewar rikici.

Kamar yadda lamarin ya kasance a majalisar an samu tayar da hakarkari lokacin mahawara game da rahoton da shugaban hukumar sauraren korarin jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta ta Jihar Kano.

Ya zuwa yanzu ana iya ganin jami’an tsaro birjik a kwaryar Kano don kwantar da hankalin al’umma da yin kariya gare su daga bata-garin da ka iya taso da fitina. Tuni dai aka iza tawagar tsohon sarki Sanusi zuwa wani garin da za a bayyana ko ina ne nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here