Isah Ahmed Daga Jos
KARAMAR Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta dauki nauyin koya wa daliban karamar hukumar, guda 1500 yadda za su rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB, ta wannan shekara da za a gudanar. Shugaban kwamitin da ya gudanar da wannan aiki, kuma tsohon shugaban makarantar sakandiren kimiyya ta Mahez da ke garin Saminaka, Malam Abubakar Ali ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce ganin yadda hukumar jarrabawar shiga jami’a ta JAMB, ta mayar da jarrabawar ta zama ta hanyar na’urar kwanfuta, kuma ganin yadda abin yake wahalar da dalibai, ya sanya shugaban Karamar Hukumar Lere Alhaji Abubakar Buba ya dauki nauyin a koya wa daliban wannan yanki, yadda za su rubuta wannan jarrabawa ta hanyar kwanfuta.
Ya ce a baya sun yi iyakar kokarinsu wajen ganin an sami wadanda za su taimaka wa daliban wannan yanki, domin su sami ilmin kwanfuta da za su yi amfani da shi wajen rubuta wannan jarrabawa, amma abin ya gagara.
‘’Shi ne shugaban Karamar Hukumar ya amince ya tallafa wa daliban, duk da cewa hakkin makarantun firamare ne yake kan karamar hukuma. Amma tun da wadannan yara ‘yan karamar hukuma ne, ya ce zai bayar da gudunmawa wajen ganin an karantar da su yadda za su rubuta wannan jarrabawa. Domin su sami cin jarrabawar, su sami tafiya manyan makarantun kasar nan’’.
Ya ce kafin su kaddamar da shirin, sai da suka yi zama da daraktan ilmi na makarantun sakandire da shugabannin makarantun sakandire da kansilolin karamar hukumar, suka yi masu bayani kan manufar shirin.
Ya ce sun debo yara guda 100 daga kowace mazaba ta wannan karamar hukuma. Kuma sun karantar da daliban a manyan makarantun sakandire guda 20 da ke wannan yanki. Sannan kuma sun yi shirin wayar da kan dalibai na bai daya, a dukkan mazabun karamar hukumar.
Malam Abubakar ya yi bayanin cewa babu shakka wannan shiri, zai taimaka wa daliban karamar hukumar, wajen cike gudaraben da ake ware masu a manyan makarantun kasar nan.
Ya yaba wa shugaban karamar hukumar, kan kokarin da ya yi wajen daukar nauyin gudanar da wannan shiri.