Jabiru A Hassan, Daga Kano. Al'umar jihar kano sun bayyana cewa nadin da gwamna Ganduje yayi wa Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin kano ya kawo inganci a bangaren sarautar gargajiya a jihar musamman ganin cewa yanzu ahalin gidan Bayero ne zai jagoranci masarautar kano. Sunyi wannan tsokaci ne a tattaunawa daban-daban da suka yi da wakilin mu inda kuma suka nunar da cewa yanzu ne jihar kano da Nijeriya zasu sami karin daraja da ci gaba duba da yadda sabon sarki Aminu Ado Bayero yake da kwarewa wajen yin aiki da hankali da kuma sanin ya kamata. Alhaji Abubakar Magaji daga yankin karamar hukumar Gwale yace ko shakka babu, Alhaji Aminu Ado Bayero jagora ne mai hangen nesa da kaunar al'uma saboda tarbiyyar da ya tashi da ita daga mahaifin sa, marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, sannan kuma baya kyamar mutane duk da irin matsayin da ubangiji ya bashi. Shima a nasa tsokacin, mai unguwar Dan Rimi Alhaji Musa Sani ya bayyana cewa sabon sarkin kano zai yi amfami da ilimin sa wajen samar da hadin kai a jihar kano musamman tsakanin masarautun jihar da ita kanta gwamnatin kano ta yadda al'amura za su ci gaba da tafiya kamar yadda ake bukata, inda yayi fatan alheri ga sarki Aminu Ado Bayero bisa wannan daukaka da Allah ya bashi. Da yake nasa tsokacin, wani dan kasuwa Alhaji Muktar Garba yace gwamna Ganduje yayi abin da ya kamata wajen farfado da sarautar kano musamman dawo da tsatson gidan Bayero a matsayin Sabin sarkin Bichi wanda kowa yayi murna da yin hakan, sannan ya sanar da cewa ko shakka babu yanzu me sarakunan kano 5 zasu had a karfi waken ganin jihar ta kara samun nasarori ta kowane fanni. Daga karshe, dukkanin wadanda suka zanta da Gaskiya Tafi Kwabo sun Isar da sakon su na fatan alheri ga gwamna Ganduje da majalisar dokikin jihar kano da kuma dukkanin wadanda suka taka rawa wajen dawo da martabar masarautar kano da sarautar gargajiya cikin nasara.