Kungiyar NRI Ta Mika Sakon Fatan Alheri Ga Sarki Aminu Ado Bayero.

0
588
Jabiru A Hassan, Daga Kano.


KUNGIYAR farfado da martabar arewa watau "Northern Reformation Initiative" (NRI) ta mika sakon ta na fatan alheri ga sabon sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa nada shi da gwamnatin jihar tayi tareda fatan cewa hakan zai kara kawo cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Abubakar Adamu ya Sanyawa hannu kuma aka rabawa maneman labarai jiya  Talata, kungiyar ta NRI ta bukaci al'umar jihar Kano da su ci gaba da baiwa Sabon sarkin goyon baya da kauna kamar yadda suka baiwa mahaifin sa marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Sanarwar race" kowa dai yasan cewa mulki na Allah ne, don haka yana dakyau ayi biyayya ga dukkanin wanda Ubangiji ya baiwa jagoranci ta yadda zai sami damar yin shugabanci na adalci kamar yadda ake fata, sannan kungiyar zata ci gaba da aikin tabbatar da hadin kai da kaunar juna tsakanin arewaci da kudancin wannan kasa Nijeriya". Inji Kungiyar.

A karshe, kungiyar na Northern Reformation Initiative tana mai fatan alheei ga gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da take yi na kawo ci gaba mai ma'ana a fadin jihar Kano ta kowane fanni.

 


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here