Ni Ba Budurwar El-Rufai Ba Ce – Hadiza Usman

0
469

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAR hukumar tashar jiragen ruwa NPA, Hadiza Usman, ta karyata zargin da ake mata na cewar tana soyayya da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kuma wai hakan ne yasa aka bata matsayin shugar NPA.

Hadiza Usman, wacce ta kasance shugabar ma’aikatan gwamnatin El-Rufai daga shekara ta 2015 zuwa 2016, ta bayyana hakane a wani hira da ta yi da gidan talabijin na TVC ranar Litinin, ranar murnar zagayowar ranar mata ta duniya.

Ta ce zargin da ake mata na soyayya da El-Rufai, labarin kanzon kurege ne wanda ya dade yana yaduwa.

“Ni ba budurwasa ba ce, Gwamna El-Rufa’I shugabana ne kuma jagorana ne.”

“Ya taimaka mun matuka wurin cimma burina da burin ko wacce mace data yi aiki a karkashinsa”

“Kamar yadda kuka sani, Jihar Kaduna ita ce jiha ta farko da aka fara zaben mace ta zama mataimakiyar gwamna, to a nan za ku iya ganin cewa yana da son ya sa mata a matsayi mai girma ta yadda za a rage yada jita jita,” A cewarta

Hadiza Usman mai kimanin shekaru 44, yar siyasa ce kuma yar fafutukan kungiyar kira da a dawo da yan matan Chibok ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada ta a matsayin shugabar hukumar tashar jiragen ruwa a watan Yuli shekarata 2016. Nadin nata ya jawo cece ku-ce a wurin jama,a cewar bata dace da matsayin ba.

Shugabar, har ila yau, ta ce wannan yunkuri ne na karya wa mata gwiwa da suke da matsayi babba.

“W annan shine abin da suke cewa mata dansu karya mana gwiwa, duk abinda kayi don nuna bajintarka akan aikinka, sai su jingina shi da cewa kana da alaka da wani ne,”

“Abin nufi a nan shi ne, ka samu aiki kuma kana aiwatarwa yadda ya kamata, toh idan mutane suka fara cewa ka samu matsayin ne saboda kai budurwar wani ce, toh wannan shi ake kira da karya gwiwa,”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here