Wurin Da Aka Kai Tsohon Sarkin Kano Kauye Ne -Sarkin Loko

0
855
Mustapha Imrana Abdullahi
ABUBAKAR Ahmad Sabo Loko, shi ne  mai martaba Sarkin Loko a Jihar Nasarawa da ke Arewacin tarayyar Nieriya ya bayyana wurin da aka kai tsohon sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi a matsayin kauye.
Mai martaba sarkin na Loko ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta muryar Amurka Sashen hausa, inda ya ce Loko nan ne aka ajiye tsohon sarkin Gwandu Almustapha Haruna Jokolo lokacin da aka cire shi daga sarautar Gwandu.
Saboda haka ya ce wurin nan hakika kauye ne don haka yana da kyau a san haka, saboda haka koda shi tsohon Sarki haruna Jokolo sai daga baya aka mayar da shi Kaduna.
Sai ya yi kira ga daukacin wadanda keda iko a kan wannan lamarin da su san cewa wurin fa wato Loko kauye ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here