Gwamnan Yobe Ya Nada (NAN) A Matsayin Darakta Janar Na ‘Yan Jaridu Da Yada Labaransa

0
372
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
GWAMNAN Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya nada wakilin kamfann dillancin labarai na kasa (NAN) Alhaji Mamman Muhammad a matsayin Darakta Janar na ‘yan Jaridu da yada labarai (DG) nasa.
Sanarwar hakan na kunshe cikin takardar dake dauke da sa hannun sakataren yada labarai na Sakataren gwamnatin Jihar Shuaibu Abdullahi da aka rarraba wa ‘yan jaridu a garin Damaturu.
Kafin nada shi wannan matsayi Alhaji Mamman Muhammad shine wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Jihar Yobe.
Kamar yadda bayani yake wannan nadi da aka yiwa Alhaji Mamman Muhammad a matsayin DG ya fara aiki ne nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here