An Ba Da Umurnin Rufe Makarantun Allo Da Islamiya A Jihar Kano

0
428

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Kano ta bayar da umurnin rufe dukkan makarantun boko, Islamiyya da na allo daga ranar Litinin, 23 ga wata, domin hana yaduwar kwayar cutar coronavirus da ta addabi duniya .

Shugaban makarantun Kur’ani, Islamiyya da Tsangaya, Sheikh Yahuza Gwani Dan Zarga, ya tabbatar da rufe makarantun ga manema labarai ranar Lahadi a Kano.

A cewarsa, umurnin rufe makarantun ya biyo bayan shawarar da gwamnonin jihohin arewa ta yamma suka yanke na rufe dukkan makarantu domin takaita haduwar mutane wuri saboda dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus.

“Ana umurtar dukkan makarantun Kur’ani, Islamiyya da Tsangaya a kan su rufe makarantu daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris, kamar yadda gwamnatin jiha ta umarta ,” a cewarsa.

Gwani Yahuza ya ce bayar da umurnin rufe makarantun tsangaya guda 12 da ke jihar Kano ba yana nufin dakatar da harkokin koyarwa ba ne, an dauki matakin ne domin kare jama’a daga kamuwa da kwayar cutar COVID-19.

“Muna kira ga shugabannin addini da sauran jagorori a kan su tashi tsaye da addu’o’i domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen annobar coronavirus ,” a cewar Gwani Yahuza.

A ranar Juma’a ne gwamnatin jihar Kano ta bayar da umurnin rufe dukkan kanana da manyan makarantunta na tsawon kwanaki 30 saboda annobar kwayar cutar coronavirus. Sai dai, jama’a da dama na tunanin cewa umurnin bai shafi makarantun Kur’ani, Islamiyya da Tsangaya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here