An Rufe Masallacin Kasa Na Abuja

0
419
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKAMAKON irin matsalar da ake kauce wa faruwarta ta fuskar yada cutar da ke toshe numfashi ta (Covid 19) Korona bairos ya sa hukumar gudanarwar babban masallacin kasa da ke Abuja suka bayyana rufe masallacin da a yanzu ba za a gudanar da salloli biyar da ake yi a masallacin ba.
Hukumar gudanarwar ta bayar da sanarwar ne a yau Litinin 23 ha watan Maris, 2020. Inda suka bayyana a cikin wata sanarwar da hukumar gudanarwar ta masallacin suka sanya wa hannu sun bayyana cewa hatta da budaddiyar kasuwar da ke masallacin da wurin cin abinci duk an rufe su baki daya har sai abin da hali ya yi domin ba a bayyana ranar bude masallacin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here