Gwamna Buni Ya Ba Da Tabbaci Ga Al’ummar Yobe Kan Shirin Ko Ta Kwana A Cutar Corona-virus

0
406
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
GWAMNA Mai Mala Buni, ya ba da tabbaci ga alummar jihar Yobe kan cewar, gwamnatinsa ta dauki matakan koda ta kwana a yayin da duniya da kasar Nijeriya  ke fuskantar ciwon Corona Virus don ganin cutar ba ta yadu a tsakankanin al’ummaf jihar ba.
Gwamna Mai Mala ya ba da wannan tabbaci ne cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Darakta Janar na manema labarai da harkokin yada labaransa Alhaji Mamman Muhammad da aka rarraba wa manema labarai a garin Damaturu.
Don haka ne ma tun tunin Gwamnan ya ba da umurni na tanadin wurin kebe wada ya samu jarabawar kamuwa da ciwon Corona virus (Allah Ya sauwaka) da kuma tanadin kayan aiki a asibitin koyarwa na jami’ar jihar da ke Garin Damaturu.
Gwamna ya ba da tabbacin cewar gwamnati za ta ba da dukkan gudumawa da ta cancanta wajen yakar wannan anoba da ta zama alakakai ga duniya.
Don haka Gwamna Mai Mala Buni ya kirayi jama’a su sanar da jami’an kiwon lafiya da zarar an ga wani mai alamun ciwon Corona virus a yankinsu.
Ya kara da kiran mutane da so bi dokokin jami’an kiwon lafiya musaman na wanke hannu a kai-a kai.
Gwamna ya kira jama’a da su ci gaba da adduar Allah Ya kawo mana saukin wannan bala’i, amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here