Korona Bairos: Gwamnan Bauchi Ya Killace Kansa

0
458

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa tun bayan hada jirgi da ya yi da dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar coronavirus.

Mai magana da yawunsa, Ladan Salihu ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ladan ya ce “mun hau jirgi daya da dan gidan na Atiku daga Lagos zuwa Abuja, inda suka yi musabiha hannu da hannu. Tuni aka yi wa Gwamna da mu ‘yan tawagarsa gwaji. Muna fatan sakamakon gwajin zai yi kyau.”

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ne ya sanar da cewa dansa ya kamu da coronavirus.

Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twiiter.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tuni aka kai dan nasa asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ake masa magani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here