Mutane Sun Fara Tururuwar Neman Gas Na Girki

0
411
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKAMAKON wata sanarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar cewa idan har jama’a ba su natsu ba suka bi tsarin doka yadda ya dace ba saboda daukar matakan hana yaduwar cutar toshe numfashi ta Covid 19, ya sa jama’a yin hanzarin kimtsa gidajensu domin gudun hawan kaifi ko tsini.
Kamar yadda wakilinmu ya zanta da wasu da kuke ganinsu a cikin jerin tururuwar nan suna neman sayen Iskar Gas ta Girki sun bayyana wa wakilinmu cewa suna kokarin samun abin da za su ajiye ne domin gudun kota kwana, kamar yadda wadansu suka gaya mini cewa suna shirin yin zaman gida ne saboda gujewa cutar Korona birus.
Za ku dai iya ganin irin yadda jama’a ke kokarin kintsa a cikin wannan hoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here