Korona Bairos: Ma’aikata Za Su Tafi Hutu A Najeriya

0
1187

Rahoton  Z A Sada

GWAMNATIN Najeriya ta umurci ma’aikatanta da ke mataki na daya zuwa na goma sha biyu su dakatar da zuwa aiki har sai abin da hali ya yi.

Gwammnatin ta dauki wannan matakin ne a kokarin da take na takaita yaduwar annobar coronavirus.

Shugabar ma’aikatan gwamnati Dakta Folasade Yemi-Esan, ta ce wannan mataki ya zama tilas kuma doka ce ga kowanne ma’aikaci ya killace kansa a gida.

Dakta Folasade, ta ce gwmanati ta damu da tsaron ma’aikata don haka daukar wannan mataki zai taimaka wajen ganin an dakile yaduwar Covid-19 a fadin kasar.

Dokar dai za ta soma aiki daga ranar Talata kuma za ta ci gaba har sai baba ta gani, a cewar Folasade.

Sannan ta shawarci duk wani ma’aikaci da ya san bai wuce mako biyu da dawo wa daga ketare ko mu’amala da mutumin daya dawo daga kasashen da ke fama da annonbar da su killace kansu na tsawon makonni biyu.

Hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasar, ta ce ya zuwa yanzu mutum 40 ne suka kamu da annobar coronavirus a Najeriya, kuma 28 daga cikinsu a jhar Legas suke.

Wannan sabon mataki na zuwa ne bayan shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus kuma sakataren gwamnatin kasar Mista Boss Mustapha ya sanar da cewa za a rufe dukkan iyakokin kasar na tudu a yunkurin dakile yaduwar annobar.

Mista Boss Mustapha, ya ce daga wannan Litinin din har zuwa mako hudu da ke tafe, iyakokin kasar na tudu za su kasance a garkame domin hana yada cutar ta coronavirus.

A cewarsa, an dakatar da taron majalisar ministoci da ake yi duk ranar Laraba sai illa ma sha Allahu.

Mista Boss Mustapha ya shawarci dukkan mazauna Abuja da Legas su zauna a gidajensu sannan su guji halartar taron jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here