An Kashe Sojojin Najeriya Fiye Da 40 A Borno

0
554

Rahoton Z A Sada

ZAUNE-TSAYE ba ta kare ba a Najeriya, a inda ana cikin fargabar yaduwar cutar korona bairos, su kuma masu tayar da kayar baya a Najeriya sun kai hari kan wasu jerin motocin sojoji inda suka kashe fiye da soja 40.

Hedikwatar tsaron kasar ta tabbatar da lamarin inda ta ce ya faru ne a wani kwanton-bauna da ake zargin mayakan Boko Haram da yi, lokacin da sojojin suke aikin sintiri a kusa da dajin Sambisa da ke shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Tun da farko wasu rahotanni sun bayyana cewa adadin sojojin da suka rasu ya kai mutum 70.

Kwamanda Abdussalam Sani shi ne jami’in hulda da jama’a na cibiyar da ke samar da bayanai a kan rundunoni na musamman a hedikwatar tsaron Najeriya, kuma a tattaunawarsu da Ibrahim Isa ya ce rundunar sojin sama ta mayar da martani, kuma ta yi nasarar halaka maharan da suka yi kwanton-baunar.

Haka ma akwai rahotannin da ke cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu sojoji yayin da aka garzaya da sauran da suka jikkata asibiti.

Kawo yanzu ba a iya tantance harin na kungiyar Boko Haram ba ne ko kuma wata kungiya da ke kai hare hare a yankin.

A tattaunawarsu da Ibrahim Isa na BBC, Kwamanda Abdussalam Sani ya ce rundunar sojin sama ta mai da martini, kuma ta yi nasarar halaka maharani da suka yi kwanton-baunar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here