Ya Umurci Ma’aikata Su Zauna A Gidajensu, A Rufe Shaguna A Kasuwa

0
505

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna ta dauki babban mataki domin kare yaduwar annobar kwayar cutar coronavirus bayan ta umurci dukkan ma’aikatanta daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida na tsawon kwanaki 30 masu zuwa. Umurnin zai fara aiki ne daga ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kazalika, gwamnatin ta umurci duk wasu ‘yan kasuwa su rufe shagunansu. Masu shagon sayar da magani da kayan abinci kadai aka yarda su bude shagunansu a jihar.

A cikin jerin wasu sakonni da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da jami’an tsaro wajen tabbatar da cewa an yi wa dokar hana jama’a da yawa taruwa a wuri guda biyayya, musamman a coci-coci, masallatai da kuma makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da ma na addini.

Gwamnan ya shawarci jama’a da su zauna a gidajensu tare da guje wa fitowa waje matukar hakan ba dole ya zama ba, saboda halin da ake ciki na fama da annobar kwayar cutar coronavirus.

El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da hukumomin tarayya domin sa ido da kuma tabbatar da cewa jama’a sun yi biyayya ga dokokin da aka gindaya domin ganin an kare jama’a daga fada wa hatsarin kamuwa da kwayar cutar coronavirus.

Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta saurara wa wadanda aka samu suna saba umurnin gwamnati ba tare da yin barazanar cewa ba zai yi jinkirin saka dokar ta baci a jihar ba idan bukatar yin hakan ta zama dole.

A cewar El-Rufa’i, tunda coronavirus ta bulla a Abuja, akwai gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakai masu tsauri domin kiyaye shigowar kwayar cutar cikin jihar da kuma sauran jihohin
arewa, musammam yanzu da jama’a ke guduwa daga Abuja saboda tsoron coronavirus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here