Gwamna Ya Ba Da Umurnin Rufe Dukkannin Makarantun Jihar

0
418
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
GWAMNA Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya bayar da umurnin rufe ilahirin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin jihar Yobe.
Bayanin hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai, mai dauke da sa hannun kwamishina a ma’aikatar ilimi a matakin farko da na sakandire Dokta Muhammad Sani Idriss a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Ya kara da cewa, “Biyo bayan barkewar annobar cutar numfashi, mai suna ‘Corona- virus’ a duniya baki daya, kana da Nijeriya a kebance, wanda kawowa yanzu kimanin mutane 30 ne ke dauke da ita a jihohi daban-daban a kasar nan, al’amarin da ya jawo Gwamnan jihar Yobe,
Mai Mala Buni ya bayar da umurnin rufe dukkannin illahirin makarantun gwamnati hadi da na masu zaman kansu, daga ranar, 26 ga watan Maris 2020 zuwa Asabar 26 ga watan Afirilun 2020”. Kamar yadda yake a sanarwar.
Snarwar ba ta tsaya nan ba, ta kara da cewa Gwamna Buni ya yaba dangane da goyon baya tare da fahimtar da iyayen yaran da masu kula da tarbiyyar yaran ke nuna wa gwamnatin sa a irin wannan lokacin, kana kuma ya bukace su da cewa su ci gaba da addu’o’in neman Allah ya kawar wa duniya wannan babban ibtila’in da take fuskanta.
Har ila yau kuma, a cikin bayanin an bukaci baki dayan shugabanin makarantun na firamare da sakandire tare da masu zaman kansu, a karkashin ma’aikatar ilimin da cewa su aiwatar da wannan umurnin nan take, ba tare da wani jinkiri ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here