Gwamnan Bauchi Na Dauke Da Cutar Korona Bairos

0
556

Mustapha Imrana Abdullahi

YA zuwa yanzu dai bayanan da ke fitowa daga fadar gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin tarayyar Nijeriya na cewa, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed na dauke da cutar Korona bairos.

Kamar dai yadda babban mai taimaka wa Gwamnan a kan harkokin yada labarai, Muktar Gidado ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata cewa hakika Gwamnan ya harbu da cutar.

Kafin a kammala yi wa Gwamnan gwaji dai an ji shi da kansa yana cewa ya hadu da Mohammed da ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da aka yi wa gwaji aka kuma tabbatar ya harbu da cutar shi ma a ranar Lahadin da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here