Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya Ya Kamu Da Cutar Korona

0
402

Mustapha Imrana Abdullahi

BAYANAN da ke fitowa daga tarayyar Nijeriya na cewa shugaban ma’aikatan Fadar shugaban kasa Abba Kyari, ya kamu da cutar Korona bairos.

Kamar yadda bayanan ke fitowa ana kyautata taron cewa ya kamu da cutar ne a lokacin da ya kai ziyara kasashen Jamus da Misra (Egypt) domin halartar wani taron tattaunawa a kan batun kamfanin wutar lantarki, wanda babban shugaban kamfanin Furofesa James Momoh, yana cikin taron

Shugaban ma’aikatan ya halarci tarurruka da dama bayan da ya dawo daga tafiyar a satin da ya wuce.

An bayyana cewa ABBA Kyari, ya fara yin tari ne a lokacin wani taro a ranar Lahadi a fadar shugaban kasa, abin da yasa jama’a suka rika maganganun cewa ya kamu da cutar.

Bayanan gwajin nasa da ya fito ranar Talata da safe ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Korona bairos.

Shi ma shugaba Muhammadu Buhari, an gwada shi an tabbatar yana dauke da cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here