An Yi Garkuwa Da Yayan Gwamnan Bauchi Kwana 1 Da Kamuwarsa Da Korona

0
686
Gwamnan Al'umma Bala Muhammad

Daga Usman Nasidi.

A YAYIN da ake jimamin kamuwar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da annobar Corona virus ba, kwatsam sai ga wasu gungun miyagu ‘yan bindiga sun sace Yaya Adamu wanda yaya ne na Gwamnan.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da Yaya Adamu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Maris da misalin karfe 7:30 na dare a gidansa da ke Unguwar Jaki, cikin kwaryar garin Bauchi.

Wannan lamari ya faru ne bayan kimanin sa’o’i 72 da Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa daga cudanya da jama’a sakamakon mu’amalar da ya yi da wani mutumi da ke dauke da cutar Corona virus.

Daga bisani a ranar Talata aka tabbatar da Gwamnan ya kamu da cutar, bayan sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, suka gudanar a kansa ya tabbatar da hakan.

Babban hadimin Gwamnan a kan harkokin watsa labaru, Mukhtar Gidado ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga majiyarmu ta misalin karfe 9:30 yayin wata hirar tarho da ta yi da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here