Corona virus: Atiku Ya Nemi Gwamnati Ta Bai Wa Kowanne Magidanci N10,000

0
481
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin kasar Najeriya
Rabo Haladu Daga Kaduna
TSOHON mataimakin shugaban kasa  Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin shugaba Buhari ta bai wa duk wani magidanci tallafin N10,000 domin rage radadin annobar corona virus.
A nasa bangaren,Atiku ya bayar da tallafin naira miliyan 50 domin yaki da annobar tare da yin kira ga ‘yan majalisar dokokin Najeriya su dawo aiki “nan take” domin yin doka ta musamman kan bai wa ‘yan kasar tallafi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kira ne ranar Laraba.
“Yayin da muke da magidanta kusan miliyan 30 a Najeriya, ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin da za ta bai wa kowane magidanci naira 10,000 a matsayin tallafi na kayan abinci,” Atiku ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa da kansa a shafinsa na intanet.
Ya ce “kamfanin Priam Group ya bayar da naira miliyan 50 a madadina a matsayin tallafi”.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce wannan kudi wani bangare ne na kudirin dokar da majalisar tarayyar Najeriya ya kamata ta yi na musamman da ya kira “Stimulus Package Act” da zai tallafa wa ‘yan Najeriya, musamman wadanda suka yi fama da cutar.
Saboda haka ne Atiku ya yi kira ga ‘yan majalisar su dawo bakin aiki “nan take” domin yin waccan doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here