Gwamna Ganduje Ya Ba Da Sanarwar Rufe Kano

0
571

Rahoton  Z A Sada

GWAMNATIN Kano ta ce daga ranar Juma’a za ta rufe iyakokinta da nufin hana shige da fice zuwa sauran jihohin kasar ta yadda za a dakile yiwuwar baza cutar coronavirus.

Cikin sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan jihar, Abba Anwar ya fitar, gwamnatin ta ce matakin zai fara aiki ne daga karfe 12 na daren Juma’a 27 ga watan Maris.

Kawo yanzu dai ba a samu bullar cutar a jihar Kano ba, sai dai gwamnatin ta ce matakin riga-kafi ne kuma a cewarta ya shafi “wadanda su ma suke son shiga Kano ta hanyar jirgin saman Malam Aminu Kano, don haka ko matafiyi ya sauka a filin jirgin na Kano, to ba zai samu shiga cikin kwaryar birnin ba.”

Ta ce haka kuma matakin zai taimaka wajen takaita shigar baki ‘yan kasuwa zuwa jihar Kano a yanzu, daidai lokacin da ake daukar matakan rage cunkoso don kare mutane daga annobar coronavirus.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa “matakin na da tsauri amma ya zama wajibi domin hana yiwuwar baza annobar coronavirus.” kamar yadda sanarwar ta fada.

Ta kara da cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen kare jihar daga cutar ta COVID-19.

“Ya kamata mutane su bai wa jami’an lafiya hadin kai da sauran masu ruwa da tsaki domin kare jihar Kano da kasar baki daya,”

A cewar gwamnan akwai bukatar mutane su bi shawarwarin ma’aikatan lafiya na yin nesa-nesa da juna da kuma bukatar zama a gida domin kare kai daga cutar.

GandujeHakkin mallakar hotoFACEBOOK/SALIHU TANKO YAKASAI

Ya kara da cewa yawaita wanke hannu da sabulu ko da ruwa ko kuma da man tsaftace hannu na daga cikin hanyoyin kare kai daga annobar cutar inda ya jaddada cewa “abin da jami’an lafiye suke yi don ci gaban kowa ne da kuma inganta lafiyar al’umma.”

Kazalika gwamnatin ta bukaci ma’aikata da sauran al’umma su kauracewa kasuwanni idan ba ya zama dole ba sai dai gwamnatin ba ta fayyace ko matakin rufe iyakokinin ya shafi har da shiga ko fitar da kayan abinci da magunguna ba.

Gwamnatin ta kuma ce jami’an tsaro za su tallafa wajen tabbatar da ganin mutane sun bi umarnin na hana shiga ko fita daga jihar sannan kuma za ta ci gaba da sa ido kan lamarin tare da sanar da mutane halin da ake ciki a kai a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here