Rabo Haladu Daga Kaduna
JAMI’AN kiwon lafiya ne suke feshin maganin kone Virus a cikin kasuwannin jihar Kaduna, kamar dai yadda muke gani ana yi a kasashen Turawa haka shi ma Gwamna El-rufai ya sanya ake ta yi a dukkan kasuwannin jihar.
Ana sa ran ma’aikatan lafiyar da da zarar sun gama feshin cikin kasuwanni, za su shiga cikin unguwanni, lunguna da sako domin kokarin dakile cutar Corona Virus da ta fara addabar mutanan Nijeriya. Muna fatan sauran Gwamnonin Arewa za su yi koyi da hakan, musammam jihohin da suke da manyan kasuwannin da mutane ke taruwa sosai.