NAF Ta Fara Jigilar Kayan Tallafin Da Attajirin Kasar Caina Ya Ba Najeriya

0
392

Rahoton Z A Sda Da Usman Nasidi.

RUNDUNAR sojojin saman Najeriya (NAF) ta fara jigilar tallafin kayan kiwon lafiya da gidauniyar wani attajiri dan kasar Caina, Jack Ma Foundation, ta ba wa Najeriya domin yakar annobar cutar coronavirus.

NAF ta fara jigilar kayan tallafin ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Murtala Mohammed International Airport (MMIA), da ke jihar Legas zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Nnamdi Azikiwe International Airport (NMIA), da ke Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kayan tallafin sun hada da wasu akwatuna 107 da ke cike da kayan duba lafiya da suka hada kayan tiyata, kayan gano kwayar cutar corona, kayan ma’aikatan lafiya da ke duba marasa lafiya da sauransu.

Bayan isowar kayan tallafin Abuja , NAF ta damka su a hannu wakilan ma’aikatar lafiya a karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abdulazeez Mashi Abdullahi, a ranar Laraba, 25 ga watan Maris.

Da yake magana da manema labarai jim kadan baya karbar kayan tallafin, Alhaji Abdullahi ya mika godiya ta musamman ga shugaban rundunar NAF, Air Marshal Sadique Abubakar, bisa jigilar kayan a kan lokaci zuwa Abuja.

Kazalika, ya mika sakon jinjina ga dukkan sauran dakarun NAF da aka yi amfani da su wajen jigilar kayan. Ya kara da cewa tabbas kayan za su matukar kara wa kokarin gwamnati na shawo kan cutar COVID-19 armashi.

A cikin sanarwar da Air Commodore Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama’a na NAF, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa NAF a shirye take ta bayar da duk wani tallafi ga kasa domin ganin an dakile barazanar da kwayar cutar COVID-19 ke yi wa jama’ar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here