Sakamakon Gwajin Cutar Korona Ya Tabbatar Gwamnan Nassarawa Bai Dauke Da Shi

0
494

Daga Usman Nasidi.

FADAR gwamnatin jahar Nassarawa ta fitar da sanarwa game da sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta gudanar a kan gwamnan jahar, Abdullahi Sule.

Sanarwar ta tabbatar wa al’ummar jahar Nassarawa, ‘yan uwa da abokan arzikin Gwamnan da ma sauran jama’an Najeriya cewa Gwamnan ya sha, duba da cewa sakamakon gwajin ya nuna ba ya dauke da kwayar cutar Corona virus mai toshe numfashi.

Sai dai duk da wannan tabbaci da sakamakon gwajin ya nuna, Gwamna Abdullahi Sule ya dauki matain killace kansa tare da ci gaba da gudanar da aiki daga gida domin ya rage cudanya da jama’a, don gudun kada kuma ya kamu.

Sanarwar ta kara da cewa: “Idan za’a tuna, Gwamna Sule da kansa ya gayyaci jami’an NCDC zuwa fadar gwamnatin jahar domin su gudanar da gwajin cutar a kansa, amma dukkanin gwaje gwajen da aka gudanar sun nuna ba ya dauke da ita.

“Za a ci gaba da sanar da jama’a duk wani ci gaba da aka samu game da matsayin lafiyar mai girma Gwamna Abdullahi Sule.”

A hannu guda,gwamnatin jahar Nassarawa ta tabbatar sa samun wani mutumi da ke tunanin yana dauke da kwayar cutar Corona virus a tattare da shi, a asibitin kwararru da ke Lafia.

Kwamishinan kiwon lafiya na jahar ya bayyana cewa mutumin ya shiga jahar Nassarawa ne daga babban birnin tarayya Abuja don halartar daurin aure a unguwar Arikya da ke garin Lafiya, a lokacin aka gano alamun cutar.

“Da gaske ne mun samu rahoton samun wani da ake zargi yana dauke da Corona virus, da misalin karfe 5 na yamma, daga Abuja ya shigo, amma a yanzu jami’anmu sun killace shi, mun fara bin diddigin mutanen da ya yi mu’amala da su.” Inji kwamishina Baba Yahaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here