Yariman Bakura Yana Da Kyawawan Manufofi Ga Kasar Nan-YEMCO.

1
668
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
KWAMITIN bayyana manufofin Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura wanda kuma yake kokarin ganin Sanata Bakura ya amince domin yin takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara ta 2023, watau (YEMCO) ya sanar da cewa Yariman Bakura yana da kyawawan manufofi ga kasar nan a matsayinsa na shugaba mai kishin al’umma.
Shugaban kwamitin Alhaji Nura Lawan shi ne ya sanar da hakan a hirar su da wakilinmu, inda ya nunar da cewa ko shakka babu, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura yana da kishin wannan kasa idan aka yi la’akari da irin kokarin da ya yi wajen bunkasa jihar Zamfara lokacin da ya jagoranci jihar na tsawon shekaru 8.
Alhaji Nura Lawan ya kuma bayyana cewa kwamitinsu na YEMCO yana aiki dare da rana domin yin tuntubar juna da haduwa da mutane masu kishin kasa domin ganin Sanata Ahmed Sani ya amince ya yi takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara ta 2023 a matsayin mutumin da zai dora daga inda shugaba Buhari zai ajjiye cikin yardar Allah.
Haka kuma shugaban kwamitin na YEMCO Alhaji Nura Lawan ya yi albishir da cewa Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura zai kawo managarcin ci gaba a kasar nan, sannan Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa abar misali cikin kasashen Nahiyar Afirka da duniya baki daya, tare da fatar cewa mutanen Nijeriya za su dubi cancantar Yariman na Bakura wajen ba shi ragamar kasarnan.
A karshe, shugaba Alhaji Nura Lawan ya sanar da cewa YEMCO ta yi wani shiri mai kyau domin hade kan al’umar Nijeriya da bayyana sahihancin Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ta hanyoyi daban-daban ta yadda sakon zai isa ga ‘yan kasa da ke zaune a kowane sako na Nijeriya, sannan ta yi amfani da wannan dama wajen yin addu’a ta neman kawo karshen annobar cutar Covid-19 a wannan kasa da kuma duniya baki daya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here