Za a binciki Ali Nuhu, Gwanja, Giggs Da Wasu ‘Yan Fim Kan Korona Bairos

0
357

Rahoton Z A Sada Da Rabo Haladu

SHAHARARREN jarumin fina-finai, Ali Nuhu ya ce hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) za ta yi masa gwajin cutar corona virus. Jarumi Ali Nuhu tare da wasu ‘yan Kannywood biyar na daga cikin taurarin da suka samu halartar bikin karrama jarumai da aka gudanar a Legas a ranar Asabar 14 ga watan Maris 2020.

Gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga duk wandanda suka halarci bikin da su je a yi musu gwajin cutar coronavirus saboda an gano cewa akwai mai dauke da cutar cikin wadanda suka halarci bikin.

A hirar da fitaccen jarumi Ali Nuhu ya yi da BBC a daren Talata, ya ce jami’an hukumar NCDC sun same sa inda suka bukaci da ya bi su ofishinsu don yi masa gwajin cutar corona virus.

Hakazalika, ya ce sun garzaya wajen abokan sana’arsa da suka samu halartar wurin bikin karrama taurarin don su ma a debi jininsu.

Abokan aikinsa din kuwa da suka samu halartar wurin sun hada da Ado Gwanja, Abubakar Mai shadda, Hassan Giggs da wani mutum daya.

Kamar yadda Ali Nuhu ya ce, za a gudanar da binciken jininsu din ne a daren nan sannan a sanar da su sakamakonsu a ranar washegari.

A halin yanzu dai, fiye da mutane arba’in ne a Najeriya suka kamu da mugunyar cutar nan ta corona virus. A ciki kuwa har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Akwai Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da kuma Muhammad Atiku, dan hamshakin mai kudi, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP a 2019, Atiku Abubakar.

A karon farko kuwa tun bayan barkewar cutar a Najeriya, an samu mutum daya da ya riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar a ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here