Shugaba Buhari Ya Rufe Iyakokin Nijeriya Kwata

0
479

Rahoton Z A Sada

DANGANE da yadda ake ci gaba da samun karuwar mutanen da suka kamu da annobar korona bairos a Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ta ba da umurnin rufe iyakokinta na sama da tudu nan take har tsawon wata daya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa daukar matakin yunkuri ne na bullo da manufofi da tsare-tsare da kayan aikin da suka dace don tunkarar cutar da aka tabbatar da kuma wadda ake zargi a cikin gida..

Ya kuma ce ya ba da umurni sai jirgin ruwa na dakon kaya ne kadai da ya shafe sama da kwana 14 a cikin teku za a bari ya sauka a tashoshin ruwa na kasar, bayan an gwada tare da tabbatar da cewa ma’aikatansa ba su dauke da wata cuta ko kadan a jikinsu.

A cewarsa matakin na tsawon kwana 14 bai hadar da jiragen ruwa masu dakon man fetur da iskar gas ba.

Buhari ya ce a ‘yan kwanakin nan, ya samu karin haske kan halin da kasar ke ciki game da annobar Covid-19 daga hukumomi da kuma jihar Legas wadda a yanzu take da kaso mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar.

Sanarwar ta ce “duk da matakin rufe iyakokin kasar ba zai yi wa jama’ar da ke kasashen waje kuma suke son dawowa gida dadi ba, amma hakan ya zama tilas domin tabbatar da lafiyar kowa da kowa.”

Sannan gwamnatin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa domin hana bazuwar cutar zuwa wasu bangarori na kasar.

Kazalika, sanarwar ta ce shugaba Buhari ya amince a saki tallafin Naira Biliyan 10 ga gwamnatin jihar Legas wadda ke zama cibiyar annobar a Najeriya don bai wa gwamnatin jihar damar karfafa matakan yaki da annobar tare da tallafa wa sauran jihohin kasar ta fuskar bunkasa kwazonsu.

“Ba da Naira Biliyan biyar ga Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, zai taimaka wajen fadada ayyukanta da kuma samar da ma’aikatan da za su yi aiki a asibitoci da dakunan gwaje-gwaje da ke sassan kasar,” in ji Muhammadu Buhari.

“Tuni rundunar sojan saman Najeriya ta mika jiragenta ga kwamitin shugaban kasa mai yaki da annobar Covid-19, don ba da damar aiwatar da hadin kan ayyuka da k’ara inganci wajen kai dauki a fadin kasa”.

BuhariHakkin mallakar hotoFACEBOOK/ADESINA

Shugaba Buhari ya kuma ce ya ba da umurni ga Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta kasar sake dawo da ma’aikatanta da suka yi ritaya daga aiki don kara yawan ma’aikatan lafiya a daidai lokacin da kasar ke neman dauki game da wannan annoba.

Bugu da kari, shugaban ya bukaci ma’aikatan cibiyar da sauran kwararrun da ke aiki da ita amma suka tafi karo horo, to su koma aiki nan take.

Ya ce tuni rundunar sojan saman Najeriya ta aika jirage da nufin dawo da wasu kwararru ‘yan kasar da ke aiki a Afirka ta Tsakiya, ta yadda za su koma gida don bayar da gudunmawarsu don shawo kan wannan cutar ta korona bairos.

Shugaban Najeriyar ya ce suna kuma duba yiwuwar bullo da matakan tallafi da nufin sassauta radadi da wannan anoba za ta haddasa wa rayukan miliyoyin ‘yan Najeriya.

Ya ce kamar yadda kuka sani tuni aka fara kokarin bitar kasafin kudin gwamnatin tarayya, kuma za a sanar da jama’a game da duk wani tallafi da zarar an kammala bitar kasafin kudi.

Muhammadu Buhari ya kuma ya umurci ma’aikatar bunkasa masana’antu da kasuwanci da harkokin zuba jari ta yi aiki da kungiyar masu masana’antu ta Najeriya don ganin duk ayyukan sarrafa kayayyakin tilas kamar abinci da magunguna da sauran kayan kula da lafiya ba su tsaya ba a wannan lokaci.

Shugaban ya kuma bukaci al’ummar Najeriya su yi hattara da wasu mutane a cikinsu da ke neman yada firgici da kuma labarai marasa sahihanci har ma da kokarin kawo rudani a wannan lokaci.

“Jazaman ne mu saurari hukumomin gwamnati da suke da ruwa da tsaki kadai wadanda kuma suke aiki ba dare ba rana don samar da bayanai na hakika kuma masu amfani ga jama’a”, in ji Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here