Buhari Ya Jinjina Wa Elumelu, Abdussamad, Dangote, Atiku da Sauransu Kan Gudunmawar Da Suka Bayar

0
380

Rahoton Usman Nasidi Da Z A Sada

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa manyan ‘yan Najeriya da kungiyoyi da suka tashi tsaye wajen yaki da annobar Covid-19 wacce aka fi sani da corona virus.

Shugaban kasar a wani jawabi daga kakakinsa, Mista Femi Adesina a Abuja a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ya jinjina wa mambobin hukumomi masu zaman kansu a Najeriya kan hada kai da suka yi wajen yakar cutar ta Covid-19.

Ya yaba ma mutane kamar haka, Dangote, Abdulsamad Rabi’u na gidauniyar BUA, Femi Otedola, Tony Elumelu, Herbert Wigwe, Segun Agbaje da Jim Ovia na UBA, bankunan Access, GTB, Zenith kan gudunmawar Naira Biliyan daddaya da kowannensu ya bayar.

Ya kuma yaba masu kan karfafa wa sauran kungiyoyi masu zaman kansu gwiwar yin hakan.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa bankin UBA ta bayar da Naira Biliyan 5 ga Najeriya da Afrika, yayin da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi alkawarin Naira Miliyan 50.

A cewarsa, bankin First Bank na hada hannu da gwamnati, majalisar dinkin duniya da hukumomin fasaha wajen samar da mafita na koyar da akalla yara miliyan daya ta yanar gizo a shirinta na Keep Them Engaged, Keep Them Safe’.

Shugaban kasar ya kuma yaba wa sauran mutanen da suka bayar da gudunmawa, wanda ba lallai ne sun sanar da duniya ba, inda ya ce, “Allah Ya ga dukkanin abubuwan kuma zai saka wa kowa da alkhairi.”

Ku tuna a baya mun kawo maku cewa a kokarinsa na hada kai domin ganin an ci galaba a kan annobar Corona virus mai toshe numfashin dan Adam, shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Isiyaka Rabi’u ya sanar da kyautar Naira Biliyan 1 ga gwamnatin tarayya.

Hakazalika, ba ya ga tallafin tsabar N1,000,000,000 a yanzu haka Abdul Samad ya yi odar karin kayan asibiti da kuma hadi da na’urori, injina da kayan gwajin cutar Corona virus da za a yi amfani da su a jahohi guda 9.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here