Gwamna El-Rufa’i Ya Kama Malamai 2 Saboda Sallar Juma’a

0
437

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu malamai biyu sakamakon bijire wa umurnin gwamnati na hana sallar Juma’a a jihar.

Tun a makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta dakatar da sallar Juma’a da addu’o’in coci na ranar Lahadi da sauran taruka a yakin da take yi na kokarin dakile bazuwar Korona Bairos a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar ya bayyana cewa malaman da aka damke sun hada da Malam Aminu Umar Usman da kuma Malam Umar Shangei wadanda aka kama a Malali da Unguwar Kanawa.

Ya bayyana cewa abin da malaman suka yi sun keta dokar jihar da kuma umurnin da manyan malamai suka bayar. Ba a dai san kowane irin hukunci za a yi wa wadannan malamai 2 ba a halin da ake ciki a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here