NUJ Ta Yaba Da Kokarin Gwamnatin Jihar Yobe Kan Hana Yaduwar Korona Bairos

0
526
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

KUNGIYAR ‘yan jaridu (NUJ) ta kasa, reshen jihar Yobe, ta yaba da ingantattun matakan da gwamnatin jihar ke dauka na kokarin dakile cutar nan ta Covid-19 ta daukar matakin ko-ta-kwana, ta hanyar kafa kwamitin aiwatar da shirin dakile barkewar annobar kwayar cutar ta  COVID-19 abin a yaba ne matuka.

Kungiyar ta NUJ ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta aika wa manema labarai, mai dauke da sa hannun sakataren ta a jihar, Kwamared Rajab Mohammed a Damaturu, babban birnin jihar Yobe,
Daga nan sai kuma kungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da cewa ta kara daukar matakin gaggawa wajen samar da na’urorin gwajin kwayar cutar zuwa kananan hukumomin 17 dake fadin  jihar, wanda ta ce hakan zai agaza matuka wajen dakile barkewar annobar.
“Har wayau  kuma, kungiyar ‘yan jaridun ta kuma  baiwa jama’a shawara wajen aiki da matakan kariya daga cutar wadanda kwararru su ka amince ayi amfani da su irin su wanke hannu a kai a kai da sabulu, saka abin da zai rufe baki da hanci, domin dakile yaduwar cutar”.
Sakataren kungiyar a jihar ya kuma bukaci gwamnati ta samar da kayayyakin kare kai daga kwayar cutar ga ma’aikata na musamman wadanda za su gudanar ayyukan tallafa wa wadanda su ka kamu da cutar don gujewa kamuwa da ita, a lokacin da su ke gudanar da ayyukan su na yau da kullum don kar ayi baya ba zani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here