Ya Yaba Da Goyon Bayan Al’ummar Jihar Yobe Kan Dakile Annobar Dauke Numfashi

0
399
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Honarabul Mai Mala Buni, ya yaba dangane da cikakken goyon bayan da al’ummar jihar Yobe suke ci gaba da bai wa kokarin gwamnatin sa na dakile bazuwar annobar kwayar cutar Covid-19 a jihar.

Gwamna Buni ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai, mai dauke da sa hannun babban Daraktan yada labarai da hulda da ‘yan jaridu a ofishinsa, Alhaji Mamman Mohammed.
Ya kara da cewa, ”Babban abin farin ciki ne bisa yadda jama’a suke bayar da hadin kai ga kwamitin da gwamnati ta kafa domin wayar da kan jama’a dangane da wannan annoba ta COVID-19; domin a gudu tare, a tsira tare”.
Alhaji Mamman ya kara da cewa, haka kuma ya yaba da yadda mutane suka dauki shawarwarin da ake basu da muhimancin gaske kan cutar Covid-19, musamman kula da wanke hanu akai, akai. .
Gwamna Mai Mala Buni ya kuma jinjina wa namijin kokarin sarakunan gargajuya, shugabanin addini tare da kungiyoyi, matasa da sauran daidaikun jama’a bisa yadda suka himmatu wajen fadakarwa da wayar wa da jama’a kai, da kuma matakan da ya kamata a dauka domin gujewa cutar.
Haka kuma, babban Daraktan ya sake shaidar da cewa, Gwamna Buni ya bika godiyar sa ga Allah madaukakin sarki, wanda a cikin buwayar sa ya kare al’ummar jihar Yobe, inda zuwa yanzu babu wanda ya kamu da wannan cutar.
Kuma ya yi kira ga al’umma da a ci gaba da addu’a Allah ya ci gaba da kare jihar Yobe daga wannan hatsabibiyar cuta ta Covid-19 dama dukkan masifu tare kuma da sauran al’ummar Nijeriya da duniya baki daya.
 Gwamna Buni ya kuma jaddada cewa gwamnatin sa a shirye take wajen daukar dukkan matakai wajen tabbatar da lafiya da jin dadin al’ummar jihar Yobe kwata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here