Za Mu Kai Wa Mutane Kayan Abinci Har Gida – Gwamnatin Legas

0
486

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Legas ta shirya bankin kayan masarufi domin raba wa gidaje 200,000 a unguwannin talakawa 377 a jihar Legas domin saukake musu radadin dokar hana fita da aka sanya domin takaita yaduwar cutar Corona virus.

Mazauna, wadanda za su fuskanci matsalar rashin abinci zasu samu kayan abinci daga gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce “Kwanaki bayan gwamnatin Legas ta bada umurnin zama a gida domin takaita yaduwar cutar Corona virus, Gwamnan Babajide Sanwoolu ya shirya wani shirin rage radadi kan talakawan jihar.”

Ba tare da bata lokaci ba, Gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, da kansa ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a hirar da yayi da manema labarai inda ya ce “Ina farin cikin sanar da shirin tattalin arziki ga mazaunanmu domin saukake radadin dokar zaman gida domin takaita yaduwar cutar #COVID19.”

“A karon farko, muna sa ran raba wa gidaje 200,000 masu adadin iyalai da ya kai shida. Za mu kara yawan ba tare da bata lokaci ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here