Amurka Za Ta Janye Mutanenta Baki Daya Daga Najeriya Saboda Annobar Corona Virus

0
420

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN kasar Amurka ta bayyana shirinta na janye duka mutanen ta baki daya daga Najeriya duk kuwa da rufe tashi da saukar jiragen sama da gwamnatin kasar ta yi
Ofishin jakadancin Amurka na Najeriya ne ya bayyana haka jiya Juma’a da yamma.

A sanarwar da ofishin ya fitar, ya bayyana cewa, ana so duka ‘yan kasar Amurka da suke Najeriya da su hallara a birnin Abuja ko Lagos, domin su samu damar bin jirgin sama da kasar ta Amurka za ta aiko. Haka kuma ta shawarci mutanen da basa biranen Abuja da Lagos din da su gaggauta bin jirgi da zai kai su biranen guda biyu kafin lokacin da kasar ta Amurka za ta gama shirye-shiryen nata.

Ta ce: “A yanzu haka babu wani jirgi da yake zuwa kasar Amurka, amma muna bakin kokarin mu wajen samar da jirgin sama da zai dauke mutanen mu duk kuwa da cewa kowacce kasa ta hana tashi da saukar jirage da shige da fice.

“Zamu aikawa da mutanen mu sako ta adireshin Email da zarar mun samu jirgin da zai dauke su.

“Yan kasar Amurka da suke da burin komawa kasarsu, ana bukatarsu da su gaggauta zuwa birnin Abuja ko Lagos.

A yanzu haka dai kasar Amurka tana dauke da mutane mafi yawa a duniya da suke da cutar Corona virus, inda yawan su ya kai kimanin mutane dubu tamanin da shida (86,000).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here