An Umurci Jami’an ‘Yan Sanda Da Ke Kwalejin Horaswa Da Su Fice Daga Bariki

0
455
IGP na 'yan sandan Najeriya

Daga Usman Nasidi.

JAMI’AN ‘yan sandan Najeriya da ke zama a barikin ‘yan sanda na horas da jami’ai masu kula da zirga-zirgan ababen hawa a kan titi, Ikeja Legas sun shiga halin fargaba bayan wani umurni daga hukumar yan sanda da ta umurci su tattara inasu-inasu su tashi daga barikin.

Majiyarmu ta bayyana cewa umurnin na kunshe ne a cikin wata takarda da ke dauke da sa hannun mataimakin kwamshina Ajewole Adebayo da kwanan watan 24 ga watan Feburairu, inda ya nemi su tashi zuwa ranar Talata, 31 ga watan Maris, ko kuma a fitar da su da karfi da yaji.

Takardar ta ce: “ Da wannan wasikar ake umurtarku ku tashi daga rukunin gidajen ma’aikata da dakunan da ke kwalejin horas da jami’an kula da zirga-zirgan ababen hawa da ke Ikeja zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2020.

“Ku sani zamanku a harabar kwalejin ya haramta, don haka idan baku tashi zuwa wannan rana ba, zaa fitar daku da karfin tuwo, kuma zaku fuskanci hukunci.”

Sai dai Yan sanda da dama sun bayyana rashin adalcin da ke tattare da wannan umurni, inda suka ce sai da suka bi duk hanyoyin da ake bi wajen neman gidajen, da kuma cika dukkanin sharuddan da ake cikawa don samu, amma kwatsam dare daya za a raba su da muhallansu.

Guda daga cikinsu, wanda ke da yara hudu ya nuna takardar da kwamandan kwalejin horas da Yan sanda ya bashi na izinin zama a gidan, don haka ya ce sun yi mamakin tashinsu da aka yi ba tare da wata kwakkwaran dalili ba.

Bugu da kari yace an fada musu wai babban sufetan ‘yan sanda ne ya ba da umurnin tashinsu, amma sun tambayi wasu na kusa da sufetan, sun tabbatar musu da cewa sufetan ba shi da masaniya game da umurnin.

Shugaban kwalejin, Adebayo a kan batun, sai ya turasu wajen mai magana da yawun Yan sandan Najeriya, Frank Mba, shi kuma bai dauki kiraye kirayen da aka yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here