Annobar Korona: Gwamnatin Filato Za Ta Rufe Iyakokin Jihar A Ranar Lahadin Nan

0
700

Isah Ahmed Daga Jos

A kokarin da gwamnatin Jihar Filato take yi, na kare yaduwar cutar annobar Kurona a jihar, zata hana zirga zirga a jihar ta hanyar rufe dukkan hanyoyin da ke shiga jihar, tun daga yau lahadi. Domin hana matafiya daga wasu jihohin shigowa jihar, har sai yadda hali ya yi. Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Abok Atu ne ya bayyana haka, a wani taron manema labarai da ya kira a gidan gwamnatin jihar, da ke garin Jos  a jiya Asabar.

Ya ce za a rufe hanyoyin da ke kan iyakokin shigowa jihar ne, don  ganin an hana shigowar matafiya daga wasu jihohi zuwa jihar da  hana zarga zargar jama’a a cikin jihar, a kokarin ganin cutar bata shigo ta yadu a jihar ba.

Farfesa Danladi Atu ya yi bayanin cewa a karin sababbin matakan da aka dauka, kan wannan al’amari, daga yanzu masu Keke Napap zasu rika daukar fasinja mutum daya ne a jihar, haka kuma masu kananan motocin haya zasu rika daukar fasinjoji mutu hudu ne, duk da direba.

Ya ce tuni gwamnatin jihar ta kafa wata  gidauniya, wadda zata rika neman taimako daga kamfanoni da sauran jama’a masu hali, don ganin an tallafawa jama’a kan halin da za a shiga, sakamakon wannan al’amari.

Ya ce a kokarin gwamnatin jihar na ganin ta kare yaduwar wannan annoba, tuni ta rufe kasuwanni da haramta bukukuwa da hana taruwar mutane fiye da 50, a garin Jos da kewaye.

Ya yi kira ga al’ummar jihar su cigaba bada goyan baya da hadin kai, kan kokarin da ake yi na ganin an kare rayukan al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here