An Tabbatar Da Samun Kwayar Cutar Korona A Jikin Sojoji 2 A Maiduguri

0
437

Daga Usman Nasidi.

DAKARUN Sojin Najeriya biyu ne aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar corona virus bayan gwajin da aka yi musu a Monguno, jihar Borno, kamar yadda jaridar Sahara reporters ta tabbatar a rahoton da ta wallafa da yammacin ranar Lahadi.

Sojojin biyu da suka dawo sansaninsu bayan sun dawo daga hutu, an killace su ne a sashi na uku na hedkwatarsu don lura da su tun ranar Asabar, 28 ga watan Maris, 2020.

Ba a tabbatar da cewa ko hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta hada da sojojin ba a cikin jimillar wadanda aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar a kasar nan ba.

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 12.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya kai mutum 96, kamar yadda kididdigar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta nuna.

Ga jerin jihohin Najeriya da aka tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus da adadin mutanen da suka kamu da ita;
1. Legas – mutum 59
2. Abuja – mutum 16
3. Ogun – mutum 3
4. Ekiti – mutum 1
5. Edo – mutum 2
6. Bauchi – mutum 2
7. Enugu – mutum 2
8. Oyo – mutum 7
9. Benue – mutum 1
10. Kaduna – mutum 1
11. Ribas – mutum 1
12. Osun – mutum 2

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here