Jabiru A Hassan, Daga Kano.
TUN lokacin da cutar Corona Virus ta bulla a duniya gwamnatocin kasashe suke daukar matakai na kariya ga al’umomin su tare da yin tanadin wuraren duba wadanda ake zaton cewa sun kamu da ita da kuma sauran matakai da hukumomi ke dauka domin dakile yaduwar cutar ta Covid-19.
A jihar kano ma gwamnati tana daukar nata matakai duba da yadda Allah ya albarkaci jihar da dumbin al’uma bisa kididdigar da akayi cewa akwai mutane fiye da miliyan goma a jihar, wanda tuni gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bi sahun sauran shugabanni wajen rufe makarantu da sassauta aikin gwamnati da kuma yin umurni a rufe dukkanin wuraren taruwar al’uma.
Haka kuma gwamnatin jihar Kano ta yi kokarin samar da wuraren duba mutane domin tabbatar da ko suna dauke da Covid-19 ko babu, sannan an rufe iyakokin jihar Kano da sauran jihohi makwabtan jihar tare da takaita zirga-zirgar ababen hawa da kuma fadakar da al’uma kan hanyoyin samun kariya daga wannan annoba ta corona virus.
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta yi wani bincike inda kuma wakilinmu ya ruwaito cewa gwamnatin Ganduje tana daukar harkar kula da lafiyar al’umar ta da muhimmanci duba da yadda take kokari sosai domin ganin ana kara dakile cutar Covid-19 wajen tabbatar da cewa kowane mutum yana bin dokokin da masana harkar lafiya suka bayar kamar yadda ake gani a fadin jihar.
Duk da cewa ba a sanya dokar ta baci ba a jihar ta Kano, amma hukumomin tsaro suna aiki dare da rana wajen ganin al’uma suna bin ka’idojin kariya daga cutar corona virus, sannan an rage cunkoson da aka saba gani musamman a manyan kasuwannin cikin birni wato kasuwar Sabon Gari da Kantin kwari da kasuwar Singa da kasuwar Kurmi da kuma kasuwar kayan abinci ta duniya da ke Dawanau.
Sannan su kansu direbobin motocin haya sun rage cusa mutane cikin mota inda kafin bullar wannan cuta akan sami mutane fiye da ka’ida a cikin mota daya, kana su kansu manyan tasoshin mota da wakilin namu ya ziyarta suna cikin yanayi mai gamsarwa yayin da filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano da tashar jirgin kasa duk suna cikin yanayi na bin umurmin gwamnati, yayin da kingiyoyin sa kai da kwararrun likitoci suka himmatu wajen fadakar da al’uma hanyoyin kariya daga cutar ta corona virus.
Bugu da kari, dukkanin gidajen kallon kwallo da gidajen taro da sauran wurare na taruwar all’uma har ma da gidajen wasannin gargajiya duk suna rufe na wucin gadi inda su kuma malamai na tsangayoyi da limamai suke kara yin addu’oi na neman kawo karshen wannan annoba a fadin duniya baki daya, tare da kara yin kira ga al’umar musulmi da su kara kokarin bautar ubangiji da neman gafarar Madaukakin sarki domin rabauta daga rahamarSa.