Babu Cibiyoyin Gwajin Kwayar Cutar Korona A Jihohin Arewa

0
650

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

HAR yanzu cibiyoyin gwajin kwayar cutar corona virus da gwamnatn tarayya ta shirya bude wa a Kano, Maiduguri, da Abakaliki ba su fara aiki ba duk da kwayar cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a kasa.

A ranar Asabar, ne cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da samun karin wasu mutane takwas da suka kara kamuwa da kwayar cutar COVID-19, lamarin da ya sauya jimillar masu dauke da kwayar cutar zuwa mutum fiye da 90, adadin zai iya karuwa kowanne lokaci, sannan ya nuna cewa an adadin masu dauke da kwayar cutar ya rubanya a cikin kwanaki biyu kacal.

Jihar Legas ce ta fi sauran jihohin Najeriya yawan adadin mutanen da suka kamu da kwayar cutar coronavirus da adadin mutane fiye da 50, sai Abuja a mataki na biyu da adadin mutane 12.

Tuni kwayar cutar corona virus ta bulla a sassa biyar daga cikin shidda na kasar nan, yankin arewa maso yamma ne kadai ba a taba samun sanarwar wani ya kamu da kwayar cutar COVID-19 ba.

Bincike ta ya nuna mata cewa har ya zuwa safiyar ranar Lahadi, babu cibiyar gwajin kwayar cutar corona virus a yankin kudu masa gabas, arewa maso yamma da arewa maso gabas.

A cikin makon da ya gabata ne ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta bude karin wasu cibiyoyin gwajin kwayar cutar COVID-19 a Kano, Maiduguri, da Abakaliki domin rage lodin da ke kan cibiyoyi 5 kacal da ke aiki yanzu.

Cibiyoyin gwajin kwayar cutar coronavirus da ke aiki yanzu a Najeriya su ne; na cibiyar NCDC da ke Abuja, asibitin kwararru da ke Irrua a jihar Edo, asibitn koyarwa na jami’ar Legas, cibiyar gwajin cututtuka masu yaduwa da ke Ede a jihar Osun, cibiyar bincike mai zurfi a bangaren lafiya da ke Legas da kuma asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar Legas.

Majiyar ta bayyana cewa har yanzu sai an yi jigilar jini zuwa Abuja daga Kano domin gudanar da gwajin cutar coronavirus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here