Usman Nasidi, Daga Kaduna.
A HALIN yanzu ta tabbata cewa Mai girma Gwamnan jihar Kaduna wato Nasir El-Rufai yana dauke da cutar COVID-19 bayan fitowar sakamkon gwajin da ya yi a kwanakin baya.
A wani rahoto bincike wanda ke nuni da irin jerin ayyukan da Malam Nasir El-Rufai ya yi kafin a gane cewa yana dauke da kwayar wannan cuta mai hana numfashi.
Mai girma Gwamna Nasir El-Rufai ya dora wa mataimakiyarsa Dakta Hadiza Balarabe nauyi a ‘yan kwanakin nan, inda ya nada ta shugabar kwamitin yaki da COVID-19 a Kaduna.
Kafin nan a ranar 18 ga Watan Maris, Gwamnan ya halarci taron gwamnonin Najeriya. Gwamnan Bauchi, Bala A. Mohammed wanda yake dauke da cutar, ya halarci wannan taro.
Washegari kuma Nasir El-Rufai ya zauna da mataimakin shugaban kasa da wasu kusoshin gwamnati da jami’an babban bankin duniya wajen taron majalisar tattalin arziki.
A Ranar 23 ga Watan Mairs, Gwamnan ya yi wani jawabi inda ya dakatar da ma’aikatan gwamnati daga zuwa ofis, ya kuma bukaci jama’a su zauna a gida na tsawon kwanaki 30.
A cikin tsakiyar makon da ya gabata, El-Rufai ya jagoranci wani taro na musamman da aka shirya domin dabbaka matakan da za a bi na rage yaduwar cutar COVID-19 a Kaduna.
Duk a wannan taro da ake yi, a kan samu tazara tsakanin manyan gwamnatin domin hana yaduwar cutar. An kuma ga Gwamnan tare da iyalinsa a gida dauke da tsummar fuska.
Har ila yau a cikin wannan makon da ya wuce, Gwamna El-Rufai ya kai ziyara zuwa kasuwar Abubakar Gummi da wasu wurare domin tabbatar da cewa jama’a suna zaune a gidajensu.