”Ina Cikin Koshin Lafiya A Killace”

0
417
Gwamnan Al'umma Bala Muhammad

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jahar Bauchi, Bala Mohammed ya jadadda cewar yana cikin koshin lafiya yayin da aka kebancesa sakamakon kamuwa da ya yi da cutar corona virus.

A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa Gwamnan na dauke da cutar ta Covid-19 wacce ta mamaye duniya musamman kasashen ketare.

Gwamna Bala Mohammed ya killace kansa tun bayan da ya yi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda aka gano yana dauke da cutar.

A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mohammed ya ce yana lafiya kuma har yanzu bai fara nuna wata alama ta cutar ba.

Gwamnan ya kuma yi godiya a kan kulawar da ya samu daga wajen mutane a wannan yanayi da ya tsinci kansa.

Har ila yau Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa za a shawo kan wannan annoba da ake ciki da izinin Allah.

Ya ce: “Assalamu alaikum. Ina godiya sosai da soyayya da kulawar da na samu a ‘yan kwanakin nan da suka gabata. Har yanzu ina killace karkashin kulawar likita. Sai dai, ina cikin koshin lafiya sannan ban nuna kowace alama ta rashin lafiya ba. Kada mu yi kasa a gwiwa wajen addu’a, za a wuce wannan lokaci ba da jimawa ba.”

Daga karshe gwamnan ya yiwa mutanen jahar Bauch da Najeriya baki daya addu’an samun rahmar Allah da kariya daga cuta, rashin tsaro da kuma talauci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here