Kasar Nijar Ta Dauke Wa Talakawa Biyan Kudin Wuta Da Ruwa

0
409

Daga Usman Nasidi.

DAGA cikin matakan hana yaduwar cutar Corona virus wacce ta addabi duniya baki daya, gwamnatin kasar Nijar ta hana fita daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a birnin Yamai inda a nan ne cutar ta fi tsanani.

Har ila yau gwamnatin ta hana shiga da fita daga birnin na tsawon makonni biyu daga ranar 28 ga watan Maris.

Shugaban kasar ta Nijar, Mohamadou Issoufou ya kuma bayar da umurnin soma farautar mutanen da ake zargin suna dauke da cutar a duk inda suke, don yi masu gwaji a cibiyoyin kiwon lafiya na cutar.

Hakazalika a kokarinta na sama wa jama’a sauki wajen samun kayayyakin da ake amfani da su wajen tsafta da kuma kashe kwayar cutar ta covid-19, gwamnatin ta soke haraji a kan irin wadannan kayayyaki da ake shiga da su kasar daga kasashen ketare, shafin labarai ta RFI ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma dauki sabbin jami’an kiwon lafiya 1500 don taimakawa wadanda ake da su a kasar a wannan hali da ake ciki.

Lura da yadda wannan cuta ta shafi harkokin yau da kullum da kuma na tattalin arziki kuwa, shugaba Issoufou, ya sanar cewa gwamnati za ta biya wa al’ummar kasar baki daya wutar lantarki da ruwan da za su yi amfani da su a watannin Afrilu da Mayun wannan shekara.

Wani sassaucin da gwamnatin kasar ta Nijar ta yi wa al’umma shi ne dakatar da karbar haraji kowane iri har sai cikin watan yuni mai zuwa, yayin da za a kaddamar da wani shirin raba wa jama’a marasa karfi abinci a matsayin kyauta, yayin da za a bullo da wani shirin sayar da abinci a kan farashi mai rahusa ga al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here