Saudiyya Ta Sanar Da Warkewar Mutum 66 Da Kwayar Cutar COVID-19

0
427

Daga Usman Nasidi.

A ranar Lahadi ne hukumar kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa wasu mutane 66 da suka kamu da kwayar cutar corona virus sun warke.

Sanarwar na kunshe ne a cikin sakon da babbar jaridar kasar Saudiyya da ake wallafa wa cikin harshen Turanci; ‘Saudi Gazette’ ta fitar ranar Lahadi.

Akwai kimanin mutum 96 da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar corona virus a kasar Saudiyya tare da asarar rayukan mutane 8.

Ya zuwa yanzu, kwayar cutar coronavirus ta kashe mutane fiye da 30,000 a fadin duniya a karshen makon nan. Kwayar cutar ta fi gigita kasar Amurka da yankin Nahiyar Turai a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

A ranar Lahadi ne kasar Andolus (Spain) ta sanar da mutuwar mutane 838 sakamakon kamuwa da kwayar cutar corona virus.

A wata kididdiga da jami’ar ‘Johns Hopkins’ ta gudanar, ta bayyana cewa mutane 30,800 ne kwayar cutar COVID-19 ta hallaka a fadin duniya, yayin da take ci gaba da mamaya da karya tattalin arzikin mutane da na kasashe.

Mutane fiye da 20,000 ne kwayar cutar ta hallaka a iya yankin Nahiyar Turai. Kwayar cutar ta kashe mutane fiye da 1400 a rana daya a kasar Spain da Italy.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here