An Gurfanar Da Wani Limami Da Wadanda Ya Jagoranta Sallah A Kaduna

0
393

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A ranar Litinin ne wata kotun Majistare da ke zamanta a kan titin Ibrahim Taiwo da ke garin Kaduna ta bayyana cewa Muhammad Umar, malamin addinin Musulunci da ya take dokar jihar Kaduna na hana jam’i, zai biya Naira Miliyan daya a matsayin kudin beli.

Umar , tare da Yusuf Hamza, Muhammad Ubale, da Auwal Shu’aibu, duk mazauna Unguwan Kanawa da ke Kaduna, an kama su da laifin hadin kai wajen karan-tsaye ga dokar jiha.

Alkali Ibrahim Musa, ya bayyana cewa Hamza, Ubale da Shu’aibu duk za a yi belinsu a kan Naira Miliyan dai-dai.

Alkalin ya bai wa masu kare kansu umurnin samar da mutum biyu da za su tsaya musu, wadanda dole su zama mazauna cikin Kaduna.

“Na ba da umurnin a tsare ku a wajen ‘yan sanda a maimakon gidan gyaran hali saboda cutar Corona virus har zuwa lokacin da za ku cika sharuddan belinku. ” Alkalin ya ce

“Wadanda za su tsaya muku dole su zama ma’aikatan gwamnati da ke matakin aiki a kalla na 14 kuma su zama sun mallaki shaida tare da asusun banki wanda akalla za a samu Naira Miliyan daya .” a cewarsa.

Tun farko dai, Daraktan gurfanarwa na jihar Kaduna, Bayero Dari, ya ce laifinsu ya ci karo da tanadin sashi na 59 da na 115 na dokokin laifukan jihar Kaduna.

Ya ce a ranar 29 ga watan Maris, wajen karfe 4:30 na yamma ne aka mayar da binciken mutanen karkashin rundunar ‘yan sanda ta musamman mai binciken manyan laifuka na jihar Kaduna wacce ke ofishin ‘yan sanda na Kawo, Kaduna.

“A ranar 27 na watan Maris ne bayani ya zo da ke bayyana cewa babban limamin Unguwan Kanawa, Malam Muhammad Umar, ya jagoranci sauran mutane uku da ke kare kansu tare da wasu mutane 17 don sallar Azahar, ” a cewarsa.

Sai dai, ya roki kotun da ta dage sauraron shari’ar don ya samu damar gabatar da shaidu.

A bukatar lauyan wadanda ake kara, Abdulbasit Sulaiman, ya bukaci kotun da ta ba da belin wadanda yake karewa.

“Ina rokon kotun nan da ta ba da belin wadanda nake karewa karkashin sashin na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

“Mun yi alkawarin za su zama masu dabi’a tagari kuma ba za su shiga abin da zai hana bincike. Zai zama babbar illa gare su idan aka mika su gidan gyaran hali “, Sulaiman ya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here