Bayan Gwajin Matan El-Rufai, An Sami Karin Mutane 20 A Legas, Abuja Da Kaduna

0
1236

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

MATAN Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, Hadiza Isma-El-Rufai da Asiya Muhammad Ahmad sun shaida wa duniya cewa sun yi gwajin wannan cuta mai yawo amma ba su dauke da ita.

Matan sun yi wannan bayanin ne a shafinsu na sada zumunta na Tuwita. Mai dakin Gwamnan sun kuma gode wa addu’o’in da jama’a suke yi masu.

Hadiza El-Rufai ta nuna cewa Gwawnan yana ta fama da zaman kadaici na kebe wa sauran jama’a, domin gudun yada wannan mummunar cuta ga sauran bayin Allah.

Isma-El-Rufai ta ce: “Na gode Jama’an Tuwita da duka addu’o’i da fatan alherinku. Mai girma Gwamna yana samun lafiya.”

Hakazalika, hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an sami karuwar mutane ashirin da suka kamu da cutar Corona virus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin ra’ayinta na Tuwita ranar Litinin inda ta ce: “An tabbatar da mutane ashirin sun kamu da #COVID19 a Najerya. 13 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Kaduna, .“

“Dai-dai Karfe 9:00 na daren 30 ga Maris, mutane 131 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami takwas, kuma biyu sun riga mu gidan gaskiya.“

Ga jerin jiha-jiha
Lagos- 81
FCT- 25
Ogun- 3
Enugu- 2
Ekiti- 1
Oyo- 8
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-2
Rivers-1
Benue- 1
Kaduna- 3

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here