Hukumar NCDC Za Ta Gina Dakunan Gwajin COVID-19 A Kano Da Jihohi 6

0
387

Daga Usman Nasidi.

MUN samu labari cewa hukumar nan ta NCDC mai takaita yaduwar cuta a Najeriya za ta kara yawan dakunan gwajin cutar Corona virus a fadin kasar nan.

Rahotanni sun zo mana a ranar Litinin cewa gwamnatin tarayya za ta gina wurare da za a rika gudanar da gwajin kwayar cutar Corona virus a jihohi bakwai.

Wadannan Jihohi su ne Ebonyi, Borno, Kano, Sakkwato, Ribas, Filato da kuma jihar Kaduna. Hukumar NCDC ta bayyana wannan ne a kan shafinta na Tuwita.
Za a gina wadannan sababbin dakunan gwajin cutar ne a ggaruruwan Maiduguri, Fatakwal, Jos da sauran manyan biranen wadannan Jihohin Najeriya da aka ambata.

Kamar yadda mu ka samu labari, NCDC za ta fara ne da ginin dakin gwajin a Garin Ebonyi domin a iya yi wa wadanda ake zargin sun kamu da cutar a Yankin gwaji.

A kaf yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta tsakiya da Kudu maso Gabas, babu inda ake gudanar da wannan gwaji na kwayar cutar COVID-19.

Da wannan shiri da gwamnatin tarayya ta ke yi, dakunan gwajin cutar za su kara yawa daga shida zuwa 13. Wannan zai taimaka wajen yakar wannan annoba.

Ana sa ran cewa za a kammala wannan aiki ne a cikin makonni uku. A halin yanzu dai akwai dakunan gwajin ne a Legas , Ibadan, Osun, Edo da kuma birnin tarayya.

A jihar Legas akwai dakunan gwajin har biyu, don haka yanzu NCDC ta yi azamar kai wannan dakunan gwaji zuwa sauran bangarori musamman Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here