Kungiyar JNI Ta Sarkin Musulmi Ta Yi Raddi Ga Malaman Da Suka Karyata Cutar Coronavirus

0
775

Daga Usman Nasidi.

KUNGIYAR jama’atu Nasrul Islam wacce ke karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta bayyana cewa jahilci ne wani malamin addini ya danganta cutar corona virus da karya.

Kungiyar ta ba da wannan sanarwar ne a ranar Litinin wacce ke dauke da jan kunne ga malaman. Ta ce suna dulmiyar da jama’a ne a kan cutar Corona virus a Najeriya.

Sanarwar da ta zama martani ga wasu rukunin malaman addinin Musulunci da suka fito suna wa’azi ga mabiyansu tare da danganta cutar corona virus da makircin yahudawa.

A sanarwar JNI din, sakataren kungiyar, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya ce bai kamata wadannan kalaman na fitowa daga bakin duk wani malamin da ya amsa sunansa ba.

Kungiyar ta bayyana takaicinta yadda wasu malaman ke wa’azi tare da yaudarar al’ummar Musulmai a kan ba su yadda akwai cutar corona virus din ba kwata-kwata.

“Ya zama dole a matsayinmu na al’umma da mu kauce wa duk wani Abu da zai maimaita abin da ya faru a Italiya inda cutar ta yi kamari. Mutane ne suka bijire wa gargadin masana kiwon lafiya a kan cutar.”

Kungiyar ta kara da nesanta kanta da abin da ta kira da karamin tunanin malamai game da duniya, wanda ta ce rashin fahimtarsa babbar illa ce ga lafiya da zai jefe al’umma cikin hatsari.

Ta kara da cewa, kamata ya yi a fahimci cewa batun annoba ba sabon abu ba ne a tarihin duniya. Ta kara da ba da misalai da dama na abubuwan da suka faru a tarihi tun zamanin Sahabbai da kuma tabi’ai wadanda suka gabace mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here