Yunwa Ta Sanya Al’umma Fandare Wa Dokar Ta-Baci A Kaduna

0
565

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A YAYINDA ake ta kokarin killace al’umma saboda gudun kara yaduwar cutar Korana Bairos ta hanyar sanya dokar Ta-baci a jahohin kasar Najeriya, wasu al’umma a garin Kaduna sun fara gajiya da zaman babu ta hanyar fandare wa bin dokar sakamakon rashin abin da za su ci duk da cewa ba a bude kasuwanni, ma’aikatu da masana’antu ba.

Wakilinmu da ya kewara wasu unguwannin da ke cikin garin Kaduna wanda suka hada da gundumar Rigasa, Tudun Wada, Sabon Tasha da kwaryar cikin garin a ranar Litinin, ya tarar da wasu al’umma na ta kai kawo domin neman abin da za su ci ko kai wa iyalansu.

A zantawarsa da wasu magidanta a cikin garin Kaduna, sun nuna alhenin rashin jin dadin su a bisa rashin kawo musu agaji na tallafi da gwamnatin jihar ta yi alkawarin rabawa wanda rashin hakan na da nasaba da kawo matsananciya yunwa wacce wasu ke ganin illar ta tafi ta cutar da ake kokarin kare al’umma daga kamuwa da ita.
Wata majiya ta bayyana cewa matsalolin sun karu ne a sakamakon rashin samun abin da za su ci a gidajensu ne duk da yake dokar ta zo ta tarar da su a yayin da suke kokarin neman abin da za su saka a bakin salatinsu domin mafi akasarin mutane na rayuwa ne hannu baka hannu kwarya.

Ta kara da cewa mutane sun sa rai da cewa a yau gwamnatin jihar za ta dan sassauta dokar don jama’a su samu damar fita neman wani dan abu duk da cewa ba lallai ba ne su samu, amma suna sa ran samun ko da dan wani abin da za su saka a bakinsu ne na wannan ranar ko abin da za su kai wa iyalansu na wannan wunin ranar.

Ta ce” Lallai mun fahimta da irin illar cutar Koronan kuma mun yarda gaskiya ne da akwai cutar, kana ana iya kamuwa da ita kai tsaye wanda hakan ya sa ita gwamnatin ta sanya wannan dokar don a kiyaye kamuwa da ita ko kara yaduwarta, don haka muna godiya ga ita gwamnatin bisa duk wani yunkuri da take domin kare al’ummarta.”

A cewar ta babu ta yadda za a yi jama’a su zauna a gidajensu sannan ga yara duk suna zaune tare da su ba dare ba rana a kan hutun dole da aka sanya su sannan babu abin da za a ba su su ci, to lallai ita kanta wannan wata cuta ce babba wacce za ta iya daga wa kowa hankali idan ba a magance ta ba ko aka sama wa jama’a wata hanyar da za a samu saukin gudanar da harkokin a yayin da suke zaune a gidajensu.

Mafi yawan jama’ar dai duk sun fito domin samun wani dan kudi a bankuna da za su iya yin wata sayayya ko neman abin da za su ci duk da kasancewa wasu masu shagunan ko kayan abinci sun ki bude wajen sana’o’in nasu balle har jama’ar su samu abin saya don amfaninsu.

Hakazalika, wasu al’umma da dama mazauna kudancin kasar da ke kokarin komawa garuruwansu, sun yi ta yin tururuwar shige da fice ta babbar hanyar shige da ficen garin na Kaduna wacce aka fi sani da titin bypass da babura hadi da manyan motoci sakamakon dokar Ta-baci wacce gwamnatin tarayyar ta sanya wa wasu jihohin kudancin kasar hadi da babban birnin tarayyar kasar wato Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here