Gwamnati Ta Sake Rage Farashin Man Fetur

0
392

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN Najeriya ta sanar da sake rage farashin man fetur zuwa Naira 123 da kwabo 50 a duk lita.

A cikin wata sanarwa da babban jami’i a sashen kula da albarkatun mai da kayyade farashin mai na kasar Abdulkadir Sa’idu, ya fitar, ya ce za a fara amfani da sabon farashin man daga 1 ga watan Aprilu, 2020.

A cewar sanarwar, an rage farashin ne bisa la’akari da yadda farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon cutar Korona Bairos.

A ranar 19 ga watan Maris, 2020, ne gwamnatin ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 145 zuwa naira 125 a duk lita.

Farashin danyen man fetur ya yi mummunar faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama a kasuwannin duniya.

Barkewar cutar Korona Bairos a duniya ya shafi yadda ake sayen man a kasuwar duniya.

Bugu da kari jayayya tsakanin Saudiyya da Rasha, ya sa man fetur din ya yi kwantai.

Masana tattalin arziki na ganin ya zama dole kasashen da ke da man su rage yawan wanda suke fitarwa kasuwannin duniya da nufin daga farashinsa.

Kazalika ana ganin rikitowar farashin man fetur din zai iya shafar tattalin arzikin kasashe da dama wadanda tattalin arzikin nasu ya dogara ga man fetur kamar Najeriya.

Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna, ta ce Najeriya za ta rasa kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarta da ta tsara za ta samu sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.

A halin yanzu dai akwai man da yawa a kasuwa, yayin da farashin ke faduwa saboda barkewar annobar Korona Bairos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here