Korona Bairos: Jami’ar Bayero Kano Ta Fara Aikin Kera Na’urar Taya Numfashi

0
414

Rahoton Z A Sada

TSANGAYAR koyon aikin injiniya ta Jami’ar Bayero Kano ta ce tana kokarin samar da na’urorin taya numfashi da ake kira ventilators don amfani da su a cibiyoyin da aka tanada wajen kebe mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta koronabairus.

Tsangayar aikin injiniyancin ta ce ta tattara wasu kwararru a fadin Jami’ar ta Bayero inda suka dukufa wajen kera na’ura guda daya da za ta zama zakaran gwaji, kafin ta tsunduma aikin samar da na’urorin da za a iya amfani da su a asibitoci.

Shugaban tsangayar aikin injiniya a Jami’ar, Farfesa Salisu Dan’azumi ya fada wa BBC cewa sun yi nisa da wannan aiki.

“Sun fara aiki har ma sun cimma kusan kashi 50 na samar da wannan na’ura,” in ji shi.

Ya kuma ce an samu samfurin na’urar ne daga irin wadda ake amfani da ita a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano kuma a cewarsa, “mako daya muka ba kwararrun domin kammala aikin samar da na’urar.”

Shugaban tsangayar ya ce duk da yake ana yajin aiki amma sun kafa kwamiti wanda ya kunshi injiniyoyi daga bangaren lantarki da na kere-kere da ma na bangaren lantarki da kere-kere gaba daya wato Mechatronics karkashin jagorancin Farfesa Abdussamad Umar Jibia.

Farfesa Salisu Dan’azumi ya ce sai an kera wannan na’ura ta gwaji sannan su sanar da jami’a don ganin inda za ta shiga ciki don zama jagora, ta yadda za a iya fadada aiki.

Annobar koronabairus dai ta sanya hatta manyan kasashen duniya irinsu Amurka da Burtaniya da Italiya shiga cikin tsananin bukatar karin kayan asibiti, saboda yawan mutanen da take shafa.

Zuwa ranar Alhamis, adadin mutanen da cutar covid-19 ta kama a cewar Jami’ar Johns Hopkins ya haura mutum miliyan daya.

Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus zuwa daren Alhamis a Najeriya ya kai mutum 184, in ji hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka.

Hukumar ta sanar da samun karin mutum 10 da cutar koronabairus ta shafa da yammacin ranar ta Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here