An Bindige Charles Tambe, Mai Tsaron gidan Abia Warriors A Ibadan

  0
  309

  Daga Usman Nasidi.

  WASU da ake zargin ‘yan daba ne sun harbi mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors, Charles Tambe a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

  An gano cewa an garzaya da Tambe zuwa asibiti mai suna University College Hospital (UCH) da ke Ibadan domin samun kulawan likitoci.

  Kungiyar ta Abia Warrior, a shafinta na sada zumunta na Tuwita, ta wallafa afkuwar labaran mara dadin ji inda ta ce: “Wasu ‘yan daba sun harbi mai tsaron gidan kungiyarmu, Charles Tambe a safiyar yau a Ibadan. Tambe yana asibiti a UCH a Ibadan yana samun kulawa.

  Mahukuntan kungiyarmu suna bin dididgin abinda ya yi sanadin afkuwar lamarin. Za mu cigaba da yi muku bayanin abinda ke faruwa. Muna bawa kowa shawarar ya guji afkawa cikin fitina.”

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here